Isa ga babban shafi
Afrika

Shugaban Algeria Tebboune ya bayyana ta kafar talabijin

A Karon farko a cikin watanni 2 shugaban kasar Algeria Abdelmajid Tebboune ya bayyana ta kafar talabijin bayan yayı jinyar cutar korona a asibitin soji dake kasar Jamus.

Abdelmadjid Tebboune, Shugaban Algeria
Abdelmadjid Tebboune, Shugaban Algeria Toufik Doudou/AP Photo
Talla

Shugaban mai shekaru 75 ya shaidawa al’ummar kasar cewar yana samun sauki, kuma yana fatar warkewa tsakanın makwanni biyu zuwa uku masu zuwa.

Tebboune na daga cikin shugabannin Duniya da suka harbu da cutar korona wada yanzu haka ta kashe mutane sama da miliyan guda da dubu 600.

Farkon shekarar bana ne dubun dubatar mutane ne suka yi tururuwa zuwa gangamin cika shekara guda da zanga zangar da ta haifar da kawar da gwamnatin shugaba Abdelaziz Bouteflika na Algeria a birnin Algiers.

Masu zanga zangar sun yi ta nuna adawar su da mulkin soji da kuma bukatar kafa gwamnatin farar hula a kasar wadda ta samu ‘yancin kai daga Faransa a shekarar 1962.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.