Isa ga babban shafi
Algeria

Jam'iyyar shugaba Bouteflika ta goyi bayan masu zanga-zanga

Jam’iyyar Shugaban kasar Algeria Abdualziz Bouteflika dake mulkin kasar, ta fito fili ta bayyana goyan bayan ta ga zanga zangar da ake yi na ganin ya sauka daga mulki da zarar wa’adinsa ya kare a watan gobe.

Shugaban kasar Algeria Abdelaziz Bouteflika.
Shugaban kasar Algeria Abdelaziz Bouteflika. AFP/File/RYAD KRAMDI
Talla

Matakin jam'yyar mai mulki, na daga cikin koma bayan da shugaban ke samu a yunkurin sa na cigaba da zama a karagar har zuwa karshen wannan shekara.

Shugaban Jam’iyyar National Liberation Front dake mulkin Algeria, Mouad Bouchareb ya fito karara inda ya bayyana cewar ba Jam’iyar ce ke mulkin Algeria ba, matakin dake nesanta Jam’iyar da shugaba Abdelaziz Bouteflika mai fuskantar bore.

Boucherab yace jam’iyyar tasu na goyan bayan juyin juya halin da al’ummar kasar ke nema, ganin yadda jama’ar kasar suka bayyana ra’ayoyin su, inda yake cewa zasu goyi bayan haka domin ganin an tattauna yadda za’a samu sabuwar kasar Algeria.

Jam’iyyar FLN ke mulkin Algeria tun bayan samun yancin kasar daga Faransa a shekarar 1962.

Ita ma babbar Jam’iyyar ‘National Rally for Democracy’ dake goyan bayan shugaba Abdelaziz Bouteflika ta caccaki matakin shugaban na cigaba da zama a karagar mulki bayan kammala wa’adin sa a watan gobe.

Jam’iyyar ta RND tabi sahun Jam’iyyun kawancen kasar da kungiyoyin kwadago da yan kasuwa da suka daina goyan bayan shugaban mai fama da rashin lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.