Isa ga babban shafi
Algeria

Kwararru da matasa kawai ne za a bai wa mukamai a gwamnatin Algeria

Firaministan Algeria Nouredine Bedoui, ya ce gwamnatin da zai kafa za ta kunshe kwararrun ma’aikata ne da suka hada maza da mata cikinsu kuwa har da matasa.

Ramtane Lamamra (Hagu) da Noureddine Bedoui (Dama)
Ramtane Lamamra (Hagu) da Noureddine Bedoui (Dama) Photo/Montage RFI
Talla

Firaministan ya bayyana hakan ne lokacin da yake gabatar da jawabi gaban jama'a cikinsu har da manema labarai a wannan alhamis, kwanaki biyu bayan da shugaba Abdelaziz Bouteflika ya nada shi a matsayin Firaminista don shawo kan tarzomar da ake yi a kasar.

Firaministan, wanda ke zaune tare da mataimakinsa Ramtane Lamamra, inda ya ce za a gudanar da taro domin tattauna matsalolin kasar, kafin daga bisani a gudanar da zaben shugaban kasa, wanda da farko ya kamata a yi shi ne a ranar 28 ga watan afrilu mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.