Isa ga babban shafi
Duniya

Facebook ya sanar da katse wasu hanyoyin sadarwa guda biyu da aka dasa a Rasha

Kamfanin Facebook ya sanar da katse wasu hanyoyin sadarwa guda biyu da aka dasa a Rasha, baya ga wata hanyar sadarwar ta daban mallakar sojin Faransa a shafinsa, inda ake zargin su da amfani da fasahar wajen katsalandan a harkokin kasashen Afrika da yankin gabas ta tsakiya.

Facebook da Google sun haramta tallace - tallacen siyasa.
Facebook da Google sun haramta tallace - tallacen siyasa. AFP/File
Talla

Facebook yace, ya datse dukkanin hanyoyin sadarwar ne saboda karya ka’idojinsa da ke hana katsalandan kan lamurran gwamnatocin kasashen ketare.

Kawo yanzu rundunar sojin Faransa ba ta ce uffam ba game da wannan zargi.

Ko a baya Shugaban shafin Facebook, Mark Zuckerberg ya shaida wa mambobin Majalisar Dattawan Amurka cewa, kamfaninsa na fafatawa da wasu mutanen Rasha da ke kokarin amfani da dandalin na facebook don cimma muradinsu.

Zuckerberg ya ce,wannan yaki ne da makami, kuma Rashawan za su ci gaba da inganta ayyukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.