Isa ga babban shafi
Algeria-Ta'addanci

Sojin Algeria sun kwato yuro dubu 80 a hannun 'yan ta'adda

Ma'aikatar tsaron Algeria ta sanar da kwato wasu makudan kudade na biyan kudin fansa daga hannun kungiyoyin ‘yan ta’adda a yankin Sahel mai fama da rikici.

Wasu jami'an tsaro.
Wasu jami'an tsaro. REUTERS/Omar Sobhani
Talla

Cikin wata sanarwa da ma’aikatar tsaron Algeria ta fitar a daren jiya Litinin, ta ce, yayin wani sumame da Sojojin suka kai lardin Jijel da ke yankin arewa maso gabashin kasar ne, suka gano makudan kudin har yuro dubu 80.

Mahukuntan Algeria dai sun bayyana ‘yan ta'addar a matsayin kungiyoyi da ke ikirarin jihadi wadanda ke tasiri a kasar tun a farkon shekarun 1990, cikinsu har da kungiyar Al-Qaeda a yankin Maghreb.

Ma’aikatar tsaron ta ce kudin da aka gano “wani bangare ne na fansar” da aka biya a wata yarjejeniya cikin watan Oktoba, inda makwabciyarta Mali ta saki wasu fursunoni 200 ciki har da shugabannin tsageru don ‘yanto wasu mutane hudu da aka yi garkuwar da su, ciki har da wata ma’aikaciyar agaji Bafaranshiya Sophie Petronin.

Kasar Algeria ta yi tir da yarjejeniyar, kuma Firaminista Abdelaziz Djerad ya ce biyan kudin fansa "na kawo nakasu ga kokarin da ake yi na yaki da ta'addanci".

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.