Isa ga babban shafi
Faransa-Mali

Akala sojojin Faransa 50 suka mutu a yakin Sahel

Shekaru 8 bayan da Faransa ta tura sojoji a kasar Mali, domin fatatakar mayakan jihadi, yanzu haka Faransa na fuskantar kalubalen yadda zata ci gaba da fada da masu ikirarin yakin addini, ba tare da ta jefa kanta cikin yakin, da zai yi wahala ta cimma Nasara.

Wasu Sojin Faransa dake yaki a Sahel
Wasu Sojin Faransa dake yaki a Sahel defense.gouv.fr/operations
Talla

Sojojin Faransa 5 ne suka rasa rayukansu a cikin wata fashewar Bam da ta faru a gefen wata hanya cikin kasar Mali yau da kwanaki 10 da suka gabata, wanda ya sa adadin sojin faransa da suka rasa rayukansu a yankin sahel ya kai 50, tun bayan ta kaddamar da hare hare, domin raba yankin arewacin Mali da mayakan dake ikrarin Jihadin Musulunci a watan janairun shekarar 2013.

Daga cikin na baya-bayan da suka rasa rayukansu sun hada ne da sergent Yvonne Huynh, mace soji ta farko da ta rasa ranta tun farkon soma kai daukin na Faransa.

Mutuwar tata ta ranar assabar, da kungiyar al-Qaïda, ta hada da harin da ya kashe wasu kauyawa 100 a jamhuriyar nijer daya daga cikin hare hare mafiya muni a yankin duk ta dau nauyi,

Wadannan mace mace, da kuma ikararin da ta musanta cewa harin jirgen sama na ranar talata da ya kashe gayyatatu mahalarta taron daurin aure su 20- sun dusar da duk wani kokarin baya bayanan da rundunar fada da ayukan ta’addanci ta kasar Faransa mai sojoji 5100 Barkhane da kuma abukan kawancenta na kasshen Afrika

Da kuma cancin huska da ta fuskanta daga al’umma a shekarar da ta gabata- kisan da Faransawan suka yi wa fitacen shugaba na kungiyar Qaïda Maghreb islamique, Abdelmalek Droukdel, kuma daya daga cikin shuwagabanin gungun dake ikararin goyon bayan musulunci da musulmi da ya yi mabayaa ga al-Qaïda.

Domin kaucewa fargabar fadawa cikin dogon rikici irin na Afghanistan, mahukumtan Paris na shirin janye karin sojojin 600 da a shekarar da ta gabata suka tura a yankin sahel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.