Isa ga babban shafi
Sahel-Ta'addanci

Interpol ta kame masu fasakwaurin da ke taimakawa ta'addanci a Sahel

Hukumar ‘yan sandan kasa da kasa ta Interpol ta sanar da kame wasu mutane da ta ke zargin ‘yan ta’adda ne dauke da nakiyoyin fasa dutse na Dynamite fiye da dubu 40 tare kuma da wasu na’urorin sarrafa nakiyoyin da dama.

Wasu jami'an tsaro da ke yaki da ta'addanci a yankin na Sahel.
Wasu jami'an tsaro da ke yaki da ta'addanci a yankin na Sahel. AFP PHOTO/ISSOUF SANOGO
Talla

Sanarwar da Hukumar ke fitarwa bayan wani sumamen hadin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya a iyakokin Mali, Nijar, Burkina Faso da kuma Ivory Coast rundunar ‘yan sandan kasa da kasar ta ce kame mutanen ya tabbatar da zargin da ta ke na cewa ayyukan hakar ma’adinan da ake ba bisa ka’ida ba, na da nasaba da ayyukan ta’addanci.

A cewar hukumar akwai kwararan hujjojin da ke nuna cewa kudaden da ake samu wajen hakar ma’adinan da ake yi a kasashen na Sahel ba bisa ka’ida ba, ana amfani da su ne wajen daukar nauyin ayyukan ta’addancin da ke ci gaba da fadada a kasashen na Sahel.

Hukumar ta ce kayakin da ta kwace daga hannun mutanen wadanda ake kyautata zaton ko dai ‘yan ta’adda ne ko kuma suna da alaka ta kai tsaye da ‘yan ta’addan, suna killace a Ofishinta, yayinda ake ci gaba da fadada bincike don gano sauran masu hannu a lamarin.

Sumamen hadin gwiwar na mako guda wanda aka gudanar da shi da nufin dakile wasu ayyukan ta’addanci a yammacin Afrika da kuma yankin Sahel a cewar Sakataren janar na Interpol Jurgen Stock ya taimaka wajen kame tarin makamai da suka kunshi bindigogi da dubbunan alburusai.

Mr Stock ya bayyana cewa, sumamen hadakar ya nuna bukatar da kasashen ke da ita na ci gaba da hadin gwiwa wajen gudanar da makamancin aikin don kawo karshen ayyukan ta’addanci da fasakwaurin mutane da na makamai baya ga na albarkatu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.