Isa ga babban shafi
Afrika

Ana ci gaba da wasannin cin kofin zakarun kungiyoyi a Afrika

A gasar cin kofin zakarun kungiyoyi Afrika, a jiya laraba 06-01-2021 kungiyar CR Belouizdad daga Algeria ta doke Gor Mahia daga Kenya da ci 6 da nema.Stade Malien daga Mali ta yi waje da Wydad Casablanca da ci 1 mai ban haushi.

Tambarin hukumar lhukumar kwallon kafar Afrika CAF
Tambarin hukumar lhukumar kwallon kafar Afrika CAF CAF
Talla

Horoya daga Guinee ta yi kunen doki daya da daya Racing Club Abidjan na Cote D’Ivoire..

Esperance daga Tunisia a fafatawar da ta yi da Al Ahly Benghazi daga Libya ,kungiyoyin biyu sun tashi ba kare bin damo.

TP Mazembe daga Jamhuriyar demokkuradiyar Congo ta doke Bouenguidi na kasar Gabon da ci 2 da 1.

V club daga jamhuriyar dimokuradiyyar Congo a fafatawa da ta yi da Young Buffaloes kungiya daga Eswatini sun tashi 2 da 2.

Eyimba daga Najeriya ta yi kasa a gwuiwa a fafatawar da ta yi da Al Merrikh daga Sudan da ci 3 da nema.

Al Hillal daga Sudan ta doke Asante Kotoko daga Ghana da ci 1 mai ban haushi.

CS Sfaxien daga Tunisia ta jib a dadi a karawar da ta yi Mouloudia Alger daga Algeriya da ci 2 da nema.

Petro Athletico daga Angola ta yi kunen doki Nkana daga Zambia 1 da 1.

Platinum daga Zambia ta doke Simba daga Tanzania da ci daya mai ban haushi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.