Isa ga babban shafi
Amurka

Magoya bayan shugaba Trump sun kutsa zauren majalisar dattijan kasar

Akalla mutane hudu ne suka rasa rayukan su a kokarin magoya bayan Shugaba mai barin gado na Amurka Donald Trump na hana zaman majalisar dattijan kasar don tabbatar da nasarar dan takara Joe Biden a zaben shugabancin kasar da ya gabata a Amurka.

Harabar majalisar Dattijan Amurka a Washington
Harabar majalisar Dattijan Amurka a Washington rfi
Talla

Gungun masu zanga-zangar da suka rika farfasa gilasan ginin majalisar dattijan Amurkan, sun hana wakilai gudanar da zaman tabbatar da shugaba Biden mai jiran gado nasarar lashe zaben kasar.

Shugaban kasar mai jiran gado Joe Biden ya bayyana cewa rashin da’a da tayar da hatsaniyar da aka gani a harabar majalisar dattawa ba ya wakiltar kasar Amurka, hakan baya nuna halayyarsu, abinda muka gani kawai shi ne wani karamin gungun masu tasttsauran ra’ayi marasa da’a da mutunci, sam abinda suka yi bai dace ba, kuma dole a kawo karshen hakan yanzu.

Biden na  kira ga wannan gungun na mutanen banza da su janye su kuma baiwa dimokaradiya damar cigaba.

Shugabanin kasashen Duniya sun mayar da martani tareda bayyana damuwa ga abinda suka kira koma baya ta fuskar dimokuradiyya a Amurka.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron a wani sako ta bidiyo a shafin sa na Twitter yayi kira ga Amurkawa.

Rahotanni daga Amurka na nuni cewa ,wasu daga cikin ministocin gwamnatin kasar  na shirin har indan ta kama tsige Donald Trump.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.