Bakonmu a Yau
Abba Sadiq kan yadda za a kawo karshen matsalolin tsaro a yankin Sahel
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:48
Gwamnatin Nijar ta jagoranci taron da ya hada dukan masu ruwa da tsaki na yankin Walam dake jihar Tillaberi mai iyaka da kasar Mali, da suka hada da sarakunan gargajiya, malamai, ‘yan siyasa da wakilan kabilun yankin mako daya baya kisan fararen hula sama da 100.Taron ya mayar da hankali ne kan yadda za a kawo karshen matsalar tsaro a yankin, lura da cewa wadanda suka jagoranci hari a kauyukan biyu ‘yan yankin ne.Kan wannan taro Salisu Isa ya tattauna da Sadiq Abba dan jarida kuma mai sharhi kan al’amuran tsaro a yankin Sahel.