Isa ga babban shafi

Dakarun Najeriya sun lalata dimbim motoci masu sulke na 'yan ta'adda

Ma’aikatar tsaron Najeriya ta ce dakarunta na sama a karkashin rundunar Operation Lafiya Dole sun lalata karin motoci masu sulke guda 7, mallakin kungiyar ISWAP masu ikirarin jihadi, wadanda suka yi yunkurin karbe sansanin sojinn kasar da ke garin Marte a jihar Borno, a arewa maso gabashin kasar.

Babban hafsan sojin Najeriya Janar Yusuf Tukur Buratai.
Babban hafsan sojin Najeriya Janar Yusuf Tukur Buratai. AFP PHOTO/STRINGER
Talla

A wata sanarwa, mai magana da yawun ma’aikatar John Enenche, ya ce wannan nasarar ta zo ne bayan wasu motoci masu sulke 7 da dakarun kasar na sama da na kasa suka lalata wa ‘yan ta’addan.

Enenche, mai mukamin Manjo Janar ya ce dakarun kasar sun yi nasarar dakile harin ta’addancin da Boko Haram da kungiyar IS shiyyar Afrika ta Yamma suka kai Marte a daren ranar 15 ga Janairu zuwa sanyin safiyar 16 ga Janairu.

Ya ce jirgin yaki mai saukar ungulu na sojin saman kasar ne ya yi ta dauki ba dadi da ayarin motoci masu sulke na kungiyar ISWAP a yayin da suke kokarin karbe sansanin soji a Marte, kuma ya samu gagarumar nasara a kansu..

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.