Sojojin Uganda sun yi ikirarin halaka mayakan Al Shebaab 189
Rundunar sojojin kasar Uganda tace dakarunta dake aikin wanzar da zaman lafiya a Somalia sun kashe mayakan Al Shebaab akalla 189 a farmakin da suka kaiwa wani sansanonin kungiyar a ranar Juma'ar da ta gabata.
Wallafawa ranar:
Dakarun na Uganda sun kaiwa mayakan na Al Shebaa farmaki ne a kauyukan Sigaale, Adimole da Kayitoye masu nisan akalla kilomita 100 daga Mogadishu babban birnin kasar.
Kawo yanzu dakarun wannzar da zaman lafiyar dake karkashin rundunar AMISOM ta kungiyar kasashen Afrika, sun shafe kalla shekaru 10 a Somalia, kuma Uganda ce kasa ta farko a Afrika da ta soma aikewa da sojojinta cikin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu