Isa ga babban shafi
Afrika-India

Afrika za ta karbi karin alluran rigakafin Coronavirus miliyan 400 daga India

Hukumar yaki da cutuka ta Afrika CDC ta sanar da yadda nahiyar ta samu karin alluran rigakafin coronavirus miliyan 400 kari kan allurai miliyan 270 da za ta karba tunda farko, ko da ya ke za ta fara da karbar miliyan 50 a watan Aprilu mai zuwa.

Allurar rigakafin Coronavirus samfurin ta India mai suna Covishield.
Allurar rigakafin Coronavirus samfurin ta India mai suna Covishield. Reuters
Talla

Sanarwar da CDC ta fitar yau Alhamis ta ce yanzu Kungiyar Tarayyar Afrika za ta karbi jumullar alluran rigakafin na Coronavirus miliyan 670 maimakon 270 da ta sanar tun da farko.

Zuwa yanzu dai galibin kasashen Afrika basu fara yiwa jama’arsu allurar rigakafin cutar ta coronavirus ba, saboda matsalar kudin sayen alluran a bangare guda kuma manyan kasashe na kokawar saye alluran don baiwa jama’arsu kariya.

Daraktan hukumar yaki da cutukan ta Afrika CDC John Nkengasong a jawabinsa gaban wani taron manema labarai, ya ce nahiyar za ta karbi alluran na Covishield miliyan 400 daga Cibiyar Serum ta India wanda ya yi amfani da fasaha iri daya da AstraZeneca wajen samar da rigakafin.

A cewar Daraktan na CDC idan aka kara alluran miliyan 400 kan allurai miliyan 270 da AU za ta karba karkashin shirin COVAX ko shakka babu za a yiwa kaso mai yawa alluran musamman a kasashe matalauta da ke nahiyar.

Tun farkon watan Janairu, CDC ta ce AU za ta karbi allurai miliyan 50 daga watan Aprilu zuwa Yuni kafin daga bisani ta karbi wasu miliyan 220 karkashin shirin COVAX.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.