Isa ga babban shafi
Sahel-Chadi

Idris Derby ya nemi taimakon kasashen Duniya don yakar ta'addanci a Sahel

Shugaban kasar Chadi Idris Deby ya bukaci taimakon kasashen duniya wajen murkushe 'yan ta’addan da suka addabi yankin. Deby ya yi wannan kira ne wajen bude taron shugabannin kasashen da ke cikin kungiyar G5 Sahel tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron wanda ke gudana a birnin N’Djamena.

Shugaban kasar Chadi yayin tattaunawarsa da Firaministan Faransa.
Shugaban kasar Chadi yayin tattaunawarsa da Firaministan Faransa. France24
Talla

Yayin bude taron, shugaba idris Deby ya ce yankin Sahel na fama da matsalar talauci, abinda ke bayar da damar ruruwar ayyukan ta’addanci.

Shugaban ya ce lokaci ya yi da kasashen duniya za su gaggauta wajen taimakawa yankin da kudade domin katse hanyar da 'yan ta’addan ke amfani da shi wajen dibar mabiya.

Taron na zuwa ne shekara guda bayan kasar Faransa ta kara yawan dakarun ta da ke yankin Sahel da zummar ganin an murkushe mayakan da ke kai munanan hare hare, amma duk da nasarar da aka samu, har yanzu 'yan bindigar na cigaba da kai hari.

Kafin fara taron majiyoyi daga Mali sun ce sojoji biyu sun mutu sakamakon taka nakiya a gefen hanya, abinda ya kawo adadin sojojin Mali da Majalisar Dinkin Duniya da kuma Faransa da suka mutu a cikin wannan shekara ya kai 29.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.