Isa ga babban shafi
Chadi-Ta'addanci

Chadi za ta kara dakaru dubu 1 da 200 a rundunar G5 Sahel don yakar ta'addanci

Shugaban Kasar Chadi Idris Deby ya bayyana shirin tura sojoji dubu 1 da 200 domin yaki da 'yan ta’adda a yankin Sahel, yayinda Faransa ke shirin rage yawan dakarun ta daga yankin mai hadari.

Wasu dakarun Sojin Chadi.
Wasu dakarun Sojin Chadi. BRHAIM ADJI / AFP
Talla

Sanarwar ta ce za a girke dakarun ne a kan iyakoki 3 da ake fama da hare hare da suka hada da iyakar Nijar da ta Mali da kuma ta Burkina Faso.

Kasar Chadi da ake ganin dakarun ta sun fi na kowacce kasa a cikin kungiyar G5 Sahel ta yi alkawarin tura sojojin ne tun a bara.

Ko a jiya Litinin shugaba Deby yayin jawabinsa a wajen bude taron shugabannin kasashen da ke kungiyar G5 Sahel tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron da ke gudana a birnin N’Djamena ya bukaci taimakon kasashen Duniya wajen murkushe 'yan ta’addan da suka addabi yankin.

Kasashen yankin na Sahel na ci gaba da fuskantar barazanar hare-haren kungiyoyin ta'addanci da na mayaka masu ikirarin jihadi musamman a Mali da Nijar wanda ke ci gaba da sarar rayukan dakaru da fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.