Isa ga babban shafi
Sudan-Habasha

Sudan ta Amince Daular Larabawa da shiga tsakani a rikicinta da Habasha

Gwamnatin Sudan ta ce ta amince da tayin Daular Larabaaw na sasanta rikicin kan iyaka da kuma batun gina madatsar ruwan da Habasha ke yi wanda ke neman haifar da yaki tsakanin kasashen biyu.

Firaministan Sudan Abdallah Hamdok.
Firaministan Sudan Abdallah Hamdok. REUTERS - HANNIBAL HANSCHKE
Talla

Kakakin gwamnatin Sudan Hamza Baloul ya ce gwamnatin rikon kwaryar kasar ta tattauna batun kuma ta amince da bukatar Daular Larabawa na shiga Tsakani.

An samu tankiya tsakanin kasashen biyu kan gina madatsar ruwan da Habasha ke yi wanda Sudan da Masar ke zargin cewar zai hana su samun ruwan sha.

Ko a jiya an ruwaito Firaministan Habasha Abiy Ahmad na bayyana cewar basa bukatar gwabza yaki da Sudan kan rikicin da ke tsakanin su, saboda haka suna bukatar sasantawa ta hanyar tattaunawa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.