Isa ga babban shafi
Mali-Faransa

Faransa tayi watsi da rahotan MDD da ya zargi dakarun ta da kisa a Mali

Gwamnatin Faransa tayi watsi da rahotan Majalisar Dinkin Duniya cewar dakarun ta sun kashe fararen hula 19 a harin sama da suka kai tsakiyar kasar Mali a watan Janairun bana.

Sojojin Faransa a karkashin rundunar Barkhane
Sojojin Faransa a karkashin rundunar Barkhane AP - Christophe Petit Tesson
Talla

Sanarwar da ma’aikatar tsaron Faransa ta fitar ya jaddada matsayin kasar dake cewa dakarun ta sun kai harin saman ne kan Yan ta’addan da aka gano kusa da kauyen Bounti a ranar 3 ga watan Janairu.

Sanarwar tace ma’aikatar na dauke da shakku da dama kann hanyoyin da aka bi wajen gudanar da binciken Majalisar Dinkin Duniyar da ya zarge ta, saboda haka ba ta ganin wannan rahoto a matsayin wanda ya gabatar da wata shaida da ta sha banban da wadda dakarun Faransa suka gabatar.

Wasu mazauna garin Bounti sun shaidawa manema labarai cewar jiragen yakin Faransa sun kai harin ne kan tawagar masu bikin aure kusa da kauyen, sabanin taron masu fafutukar jihadi kamar yadda Faransa ta sanar.

Wannan ya sa ofoshin Majalisar Dinkin Duniya dake Mali ya kaddamar da bincike kan lamarin, wanda rahotan da aka gabatar yau ya tabbatar da bikin da akayi wanda ya samu halartar mutane kusan 100 a inda jiragen Faransa suka kai harin.

Rahotan ya kara da cewar wasu mutane 5 dake dauke da makamai da ake zaton ya'an kungiyar Katiba Serma ne sun halarci bikin.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.