Isa ga babban shafi
ECOWAS - Cape Verde

Lauyoyin Afrika sun zargi Cape Varde ta rashin mutunta kotun ECOWAS

Kungiyar Lauyoyi ta Afrika ta rubuta takardar korafi ga hukumar gudanarwar kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS, inda suke neman ladabtar gwamnatin kasar Cape Verde kan kin mutunta babbar kotun kasashen na ECOWAS.

Hoton gudumar Alkali.
Hoton gudumar Alkali. © african-court.org
Talla

Cikin wasikar da ta rubuta, kungiyar lauyoyin ta Afrika ta ce korafin na ta ya biyo bayan takardar koken da ta samu daga Mis Camila Fabbiri Uwargidan jami’in Diflomasiyyar Venezuela Alex Saab da gwamnatin Cape Verde ke tsare da shi, bayan kama shi da ta yi a lokacin da jirginsu ya sauka a filin jiragen saman kasar domin shan mai, a yayin da yake kan hanyar yiwa gwamnatin Venezuela jigilar kayayyakin abinci daga kasar Iran.

Takardar korafin ta ce an kame jami’in dilomasiyyar na Venezuela ne ba tare da samun izinin kotu ba, ko kuma na hukumar ‘yan sandan duniya ta Interpol, da sauran hukumomin masu hurumin bada umarnin.

Kungiyar Lauyoyin ta kara da cewar, bayan korafin mai dakin Alex Sabb ne sashinta na kare hakkin dan adam ya gudanar da binciken da ya tabbatar da dukkanin abinda ta sanar dasu, wannan ta sanya su shigar da kara kotun ECOWAS, wadda ta yanke hukuncin baiwa gwamnatin Cape Varde umarnin yiwa jami’in diflomasiyyar na Venezuela daurin talala a gida, tare da bashi damar ganawa da lauyoyinsa da iyalansa, a maimakon tsare shi a gidan Yari, tare da biyansa diyyar dala dubu 200.

Sai dai tun ranar 15 ga watan Maris da kotun ta ECOWAS ta bada umarnin, har yanzu gwamnatin Cape Verde ba ta nuna alamun za ta mutunta shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.