Isa ga babban shafi
Chadi-Ta'addanci

Dan Idris Deby zai jagoranci sabuwar Majalisar mulkin Sojin Chadi

Dan marigayi Idris Deby Itno Janar Mahamat Deby ya karbi ragamar shugabancin Chadi bayan rasuwar mahaifinsa yau sakamakon raunukan da ya samu a gwabzawa da ‘yan tawayen FACT da ke arewacin kasar.

Marigari shugaba Idriss Deby Itno na Chadi a tsakiya tare da Dansa Janar Mahamat Idriss Deby Itno daga dama.
Marigari shugaba Idriss Deby Itno na Chadi a tsakiya tare da Dansa Janar Mahamat Idriss Deby Itno daga dama. © AFP - Stringer
Talla

A kalaman kakakin Sojin Janar Azen Bermandoa Agouna ta gidan rediyon kasar, ya ce janar Mahatma Deby mai tauraro 4 zai ja ragamar shugabancin kasar.

Tuni Rundunar Sojin ta Chadi ta sanar da rushe gwamnati da Majalisar kasar yayinda suka sha alwashin kiran sabon zabe a nan gaba.

Marigari shugaba Deby kamar yadda sanarwar Soji ta bayyana ya rasu ne bayan arangama da ‘yan tawayen FACT a fadan da dakarun kasar suka yi nasarar kasha ‘yan tawayen 300.

Tun karshen mako yayin fafatawar sanarwar ‘yan tawayen ta FACT ta nuna cewa gumurzun ya kai ga jikkatar Deby mai shekaru 68.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa har a ranakun Asabar da Lahadi Deby na yankin na Arewaci wajen yaki da ‘yan tawayen gabanin samun rauni wani lokaci bayan nan wanda ya kai ga rasa ransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.