Isa ga babban shafi
Chadi

Mahamat Idris Deby ya karbi ragamar shugabancin Chadi

Dan tsohon shugaban kasar Chadi Idris Deby, Mahamat Kaka Deby ya karbi ragamar tafiyar da kasar yau laraba a dai dai lokacin da 'yan adawa ke bayyana matakin a matsayin juyin mulki.

Mahamat Idriss Deby Itno, sabon shugaban kasar Chadi.
Mahamat Idriss Deby Itno, sabon shugaban kasar Chadi. © Tele Tchad via AP
Talla

A dafatarin da majalisar mulki ta sojin kasar suka gabatar yau ta kunshi shirin gwamnatin rikon kwaryar da za ta yi aiki na watanni 18 wajen shirya zaben sabon shugaban kasa, bayan rusa gwamnati da kuma nada Mahamat mai shekaru 37 a matsayin shugaban rikon kwarya.

Daftarin dokar sojin ya bayyana cewar Mahamat ne zai aiwatar da duk ayyukan shugaban kasa kuma shi ne babban kwamandan rundunonin sojin kasar a watanni 18 da za su kwashe suna jagorancin gwamnatin rikon kwaryar da zai shirya zabe.

Sai dai manyan jam’iyyun adawar kasar sun yi watsi da abinda suka kira juyin mulki, yayin da suka bukaci jama’ar kasar da su bijirewa gwamnatin.

Suma 'yan tawayen kungiyar FACT ta hannun kakakin su Kingabe Ogouseimi sun yi watsi da majalisar sojin inda suka ce za su cigaba da tattaki zuwa birnin N’Djamena.

Yanzu dai haka dakarun sojin kasar tare da masu tsaron fadar shugaban kasa na sintiri a babban birnin kasar domin tabbatar da tsaro, yayin da ake shirin yiwa tsohon shugaban kasar Idris Deby jana’iza ranar juma’a mai zuwa.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da shugaban kungiyar kasashen Afirka Moussa Faki Mahamat da shugabannin kasashen Faransa da Najeriya da Nijar da Mali duk sun aike da sakon ta’aziya ga mutanen Chadi kan rasuwar Deby wanda ya taka rawa wajen yaki da ayyukan ta’addanci a yankin Sahel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.