Isa ga babban shafi
Sahel-Ta'addanci

Tallafin kudin Faransa ga Sahel don yakar ta'addanci ya gaza- rahoto

Sashen binciken kudi na kotun kolin Faransa ya fitar da wani rahoto kan ayyukan soji da na farar hula da ke da alaka da tallafin da kasar ta bai wa kasashen yankin Sahel, inda rahoton sashen ke sanar da gano matsaloli wajen bibiyar yadda ake tafiyar da taimakon kudin da kasar ta bayar a fannin ayyukan tsaro da ci gaban da ke fuskantar koma bayan rashin kyakkyawan tsari.

Rahoton da sashen binciken kudi na Faransa ya fitar ya diga ayar tambaya kan idda kudaden da kasar ke baiwa yankin na Sahel ke tafiya maimakon yaki da ta'addanci.
Rahoton da sashen binciken kudi na Faransa ya fitar ya diga ayar tambaya kan idda kudaden da kasar ke baiwa yankin na Sahel ke tafiya maimakon yaki da ta'addanci. AFP - MICHELE CATTANI
Talla

Alkalumman da hukumar samar da ci gaba ta MDD da PNUD ta fitar, sun nuna cewa yankin sahel ne ya fi fama da matalauta a duniya, inda kuma anan ne aka fi samun karuwar  haihuwa a tsankanin al’umma.

Duk kuwa da cewa yankin bai rasa kudaden tallafin ci gaba ba, kamar yadda kotun binciken kudaden ta Faransa ta sanar.  

Daga 2012 zuwa 2018 Kudaden tallafin da Faransar ke bai wa kasashen yankin G5 Sahel sun rubanya gida 2, inda suka zarta miliyan 580 zuwa sama da Euro biliyan 1.3 kudaden da har zuwa yau ba su bada damar inganta rayuwar al’ummar yankin ba.

A cewar sashen binciken kudaden Faransa Matsalar tsaro ce babbar matsalar da ke haifar da tarnaki ga ci gaban kasashen kungiyar ta G5 Sahel, inda ya ce ba za a taba samun kwanciyar hankali da tsaro tare da samun ci gaban tattalin arziki inganta rayuwar al’umma da kuma tabbatar da hukumomi na gari ba.

Hare haren soji kan gungun mayaka shi kadai bai zai wadatar ba wajen samarwa al’ummar yankin na Sahel ingantaciyar rayuwa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.