An kammala taron kasashen G5 Sahel a birnin Yamai
An kawo karshen taron kasashen G5 sahel a birnin Yamai ta Jamhuriyar Nijar, bayan da aka kwashe kwanaki biyu ana tauttanawa a kan yadda za’a yi a shawo kan matsalolin tsageranci da ta’addanci a yankin tsakiyar sahel da wuraren tafkin Chadi.
Wallafawa ranar:
Domin shawon kan matsalolin tsaro da suka addabi yankin tsakiyar sahel da tafkin Chadi ne hukumar karfafa zaman lafiya HACP ta Nijar, tare da hadin gwiwar kungiyar PNUD suka gudanar da wani taron nazari a birnin Yamai.
Taron ya samu halartar manyan masana kan zaman lafiya, kuma shugaban taron, Janar abou Tarka ya ce an cimma biyan bukata a taron.
sai dai wasu matasa da suka samu lekawa zauren taron sun koka da yadda ba a ba su damar kawo tasu fusahar ba sakamakon rashin gayyatar su a hukumance.
Taron ya yi Nazari kan abubuwa uku da ke da nasaba da tsaro, kuma za a mika su ga gwamnatoci a matsayin shawarwari da za su taimaka wajen kawo karshen ta’addanci a yankin tsakiyar sahel da tafkin chadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu