Isa ga babban shafi
Somalia - Siyasa

Majalisar Somalia ta soke karin wa'adin mulki shugaban kasa na shekaru 2

‘Yan majalisar dokokin Somalia sun kada kuri’ar soke Karin wa’adin shugabanci na shekaru biyu da suka amince da shi a watan da ya gabata, bayan da wani kazamin rikici da ya barke a Mogadishu babban birnin kasar tsakanin bangarorin jami’an tsaro, wadanda suka samu rarrabuwar kawuna kan batun.

Shugaban kasar Mohamed Abdullahi Mohamed
Shugaban kasar Mohamed Abdullahi Mohamed - AFP
Talla

A jawabin da ya gabatar bayan kada kuri'a a majalisar dokoki, Firaminista Mohamed Hussein Roble ya umarci sojojin da su koma bariki sannan ya bukaci 'yan siyasa su guji tayar da rikici.

Rikicin siyasan ya haifar da fargabar cewa masu tayar da kayar baya na kungiyar al Shabaab wadanda ke da alaka da kungiyar Al Qaeda za su iya amfani da yanayin na rashin tsaro idan sojojin suka fara farwa juna.

Kungiyar ta karbe akalla kashi daya na Somaliya a cikin makon da ya gabata yayin da mayaka dauke da muggan makamai suka kaura daga karkara zuwa babban birnin kasar.

Kashen duniya sun fusata da karin wa'adin

Yunkurin Shugaba Mohamed Abdullahi Mohamed na tsawaita wa’adin mulkin sa ya fusata masu bayar da agaji na kasashen waje, wadanda suka mara wa gwamnatinsa baya a kokarin samar da kwanciyar hankali a Somalia bayan sama da shekaru 20 a matsayin kasar da ta gaza bayan yakin basasa da ya fara a 1991.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.