Isa ga babban shafi
Kamaru - 'Yan aware

Kamaru na bikin hadewar kasar da yankin da ake amfani da harshen Ingilishi

Yau ake gudanar da bukukuwan cika shekaru 49 da hadewar Kamaru a matsayin kasa daya dunkulalliya, bayan da al’ummar kasar suka kada kuri’ar amincewa da hakan a 1972.Duk da cewa an aiwatar da sauye-sauye na siyasa game da yadda ake tafiyar da kasar, to amma daga bisani an sake samun barkewar tashe-tashen hankula musamman a yankin da ke amfani da turancin ingilishi.

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya, a shekarar 2020
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya, a shekarar 2020 © Paul Biya twitter
Talla

An samar da kasar jamhuriyar Kamaru ne a ranar 1 ga watan octobar shekarar 1961 sakamakon wata yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Kamaru ta tsakkiya da kuma jamhuriyar Kamaru mai cikakken yanci tun ranar 1 ga watan janairun 1960  tun daga wancan lokacin ne tsarin siyasar kasar Kamaru ya fuskanci sauye sauyen da ya kai ga hadewar kasar waje guda a 1972.

Bangaren da ke karkashin Jamus da Burtaniya

Manufar samar da tarayyar kasar ta Kamaru dai  ta zo ne karkashin sha’awar da 'yan kasar suka nuna na son rayuwa tare, a lokacin da kasar ke karkashin mulkin mallakar kasar Jamus karkashin wata yarjejeniya da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya a Kamaru ta Birtaniya inda yankin kudancin kasar ya amince ya hade da yankin gabashi. 

A ranar 26 zuwa 28 ga watan yunin 1961 ne aka gudanar da taron Bamenda, manufar taron kuma ita ce  shirya tattaunawa da mahukumtan kamaru ta gabas domin hade kasar.

A ranar 16 zuwa 21 ga watan yulin 1961 ne kuma aka gudanar da taron Foumban bisa manufar rubutawa tare da amincewa da kundin tsarin mulkin tarayyar kasar ta kamaru.

A yayin da a watan Ogustan 1961 zaman taron Yaounde da ya kamata ya tantance yan Kamaru da suka shiga aiki sojin a Najeriya, domin sassaka su ma’aikatu daban daban  a kasar ta Kamaru ya kammala.

Tsohon shugaba Amadou Ahidjo

Bayan gudanar da duk wadannan taruka ne Amadu Ahijo shugaban hadadiyar kasar ta Kamaru na farko  ya ziyarci Buea a ranar 30 ga watan September 1961 inda ya karbi yancin cin gashin kan kamaru ta tsakiyar ga kasar Ingla,

A  yayin da a ranar 1 ga watan october 1961 wannan yanki na Kamaru mai cin gashin kai, ya hade da na gabashi, duk kuma a rana guda  aka samar da  jamhuriyar tarayyar kasar Kamaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.