Isa ga babban shafi
Kamaru - 'Yan tawaye

Wata kungiya ta yi barazanar kaddamar da hare-hare kasar Kamaru

Wata sabuwar kungiyar ‘Yan Tawaye a Kasar Kamaru da ta kira kanta da na ‘Yanto kasar ce, MLC ta yi barazanar fara kaddamar da hare-hare kan gwamnatin Yaounde, sakamakon abin da ta kira mulkin Kamakaryar Paul Biya na kussan shekaru 40, tare da alakanta kanta da wata kungiyar arewacin kasar da gwamnati ta haramta a baya-bayan nan.

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya Ludovic MARIN / AFP
Talla

A cikin wani sakon bidiyo da jaridar Cameroon Infonet ta walllafa a Intanet ne, kungiyar ta Movement for the Liberation of Cameroon MLC, ta yi barazanar fara kaddamar da hare-hare babban birnin kasar Yawunde da sauran sassa

Cikin hoton bidiyon na tsawon mintuna 12,  wani mutum sanye da kakin sojo, kewaye da wasu mukarrabansa suma cikin kayan na sarki dauke da makamai a wani daji, ya bukaci sakin wasu manyan ‘yan siyasa da gwamnati ke tsare da su tsawon shekaru ciki harda tsohon ministan cikin gidan kasar Marafa Hamidu Yahaya.

Mutumin dake Magana cikin harsunan Faransanci da kuma Fulatanci ya gargadi kauyawan yankin da kada su kuskura su tsokanesu domin kuwa su da gwamnati suke ba da fararen hula ba, amma muddun suka taba su, to zasu gane kurensu, yana mai cewa gwamnati na kokarin hada ‘yan banga domin a yake su.

MLC ta kuma yi tsokaci dangane da rusa wata kungiyar arewacin kasar da ake kira 10 miliyan Movement, da wani fitaccen dan jarida Gaibai Gitama ya kafa, saboda kare muradun yankin, to sai dai, shugaban kungiyar ya nesanta kansa da duk wani alaka da ‘yan tawayen.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.