Isa ga babban shafi
Najeriya-Chadi

Buhari ya nemi agajin Amurka da Faransa don dawo da mulkin farar hula a Chadi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci taimakon kasashen Faransa da Amurka da kuma Majalisar Dinkin Duniya wajen ganin an samu mika mulki ga fararen hula a Chadi cikin kwanciyar hankali sakamakon rasuwar shugaba Idris Deby Itno.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin ganawa da shugaban mulkin Soji na, Mahamat Idriss Déby a Abuja.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin ganawa da shugaban mulkin Soji na, Mahamat Idriss Déby a Abuja. AFP - SUNDAY AGHAEZE
Talla

Rasuwar shugaba Idris Deby Itno ta haifar da damuwa kan zaman lafiyar Chadi wanda sojojin ta ke taka gagarumar rawa wajen yaki da Yan ta’adda a Yankin Sahel da kuma Tafkin Chadi.

Sojojin Chadi sun taka rawa wajen taimakawa Najeriya kawar da mayakan boko haram daga yankunan arewa maso gabashin kasar a shekarar 2015, yayin da suka yi ta bada gudumawa akan iyakokin kasashen.

Gwamnatin mulkin sojin Chadi dake karkashin Janar Mahamat Deby ta nada majalisar mulkin rikon kwarya da zata mika mulki bayan watanni 18 bayan gudanar da zabe.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jaddada muhimmancin goyan bayan gwamnatin Chadin wajen ganin ta cika alkawarin da tayi a cikin watanni 18, inda ya bukaci mutunta kundin tsarin mulkin kasar.

Buhari ya bukaci kasashen Faransa da Amurka da Birtaniya tare da Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar kasashen Turai da su taimakawa kasar wajen cika alkawarin da tayi.

Shugaba Deby ya rasu ne ranar 19 ga watan Afrilu sakamakon raunukan da ya samu a fafatawar da suka yi da dakarun Yan tawayen FACT dake da sansani a kasar Libya.

A karkashin mulkin Deby, Chadi dake da daya daga cikin rundunar soji mai karfi a Afirka ta Yamma, tat aka rawa sosai wajen yaki da boko haram da kungiyar ISWAP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.