Kungiyar AU ta bukaci shugabancin mulkin Soji a Chadi ya cika alkawari
Kungiyar kasashen Afirka ta AU ta bukaci shugabannin mulkin sojin Chadi da su tabbatar da mika mulki ga fararen hula a cikin watanni 18 masu zuwa bayan sun karbi ragamar tafiyar da kasar sakamakon rasuwar shugaba Idris Deby.
Wallafawa ranar:
Sanarwar kungiyar ya bayyana rashin amincewar sa da duk wani yunkuri na kara wa’adin gwamnatin Sojin bayan kammala watanni 18.
Majalisar mulkin sojin da ke karkashin Janar Mahamat Deby, wanda ‚da ne ga marigayi shugaban kasar, ta kafa majalisar mulkin da ta kunshi sojoji da fararen hula, yayin da ta sanar da murkushe 'yan tawayen da ake zargi da kashe tsohon shugaban kasar.
Deby da ya jagorancin Chadi na shekaru 30 ya rasu ne sakamakon harin da 'yan tawayen FART suka kaddamar akan dakarun gwamnati.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu