Isa ga babban shafi
Chadi - 'Yan tawaye

Sojojin Chadi sun yi shelar samun nasarar murkushe ‘yan tawaye

Sojojin Chadi sun yi shelar samun nasara kan mayaka ‘yan tawayen kasar, bayan kwashe wata daya chur suna fafatawa dasu.

Wasu sojojin kasar Chadi.
Wasu sojojin kasar Chadi. ASSOCIATED PRESS - Jerome Delay
Talla

A ranar Lahadin nan da ta gabata  a birnin N'Djamena sojan kasar suka gabatarwa manema labarai jerin ‘yan tawaye 156 da suka kame.

Dakarun na Chadi sun kuma yi baje kolin tankunan yakin da suka kama yayin gumurzun da suka yi da ‘yan tawayen.

Fadan da dakarun na Chadi suka gwabza da ‘yan tawayen a baya bayan nan ne dai yayi sanadin mutuwar shugaban kasar Idris Derby Itno a watan Afrilun da ya gabata.

Tsohon shugaban kasar Chadi marigayi Idris Deby Itno a tsakiyar dakarunsa.
Tsohon shugaban kasar Chadi marigayi Idris Deby Itno a tsakiyar dakarunsa. ASSOCIATED PRESS - Jerome Delay

Ranar 11 ga watan Afrilun da ya gabata, ‘yan tawayen kungiyar FACT da babban sansaninsu ke Libya, suka kaddamar da farmaki kan dakarun Chadi a daidai lokacin da aka soma zaben shugaban kasa.

Bayan barkewar sabon fadan ne, tsohon shugaba Idris Deby ya jagoranci sojojin Chadi da zummar murkushe ‘yan tawayen, sai dai ranar 19 ga watan na Afrilu rundunar sojin kasar ta sanar da mutuwarsa sakamakon raunukan da ya samu yayin fafatawa da masu tayar da kayar bayan a yankin na Kanem dake gaf da iyakar Jamhuriyar Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.