Burkina Faso ta karbi alluran rigakafin corona dubu 115 daga MDD
Gwamnatin Burkina Faso ta sanar da karbar allurar rigakafin corona dubu 115 da 200 a karkashin shirin Majalisar Dinkin Duniya na taimakawa kasashe matalauta domin yaki da cutar.
Wallafawa ranar:
Ministan lafiya Charlemagne Ouedraogo ya bayyana farin cikin kasar na karbar kashi na farko na allurar, wanda ya ce zai taimaka musu wajen yaki da cutar.
Ouedraogo ya ce a ranar laraba mai zuwa za su fara gabatar da allurar ga jama’a, kuma za a fara mayar da hankali ne kan mutanen da suka fi bukatar maganin, tare da jami’an kula da lafiya da kuma maniyata aikin hajjin bana.
Burkina Faso na fatar yiwa kashi 3 na al’ummar kasar miliyan 20 allurar daga cikin mutane miliyan 10 da ake fatar ganin sun samu maganin.
Ya zuwa yanzu mutane dubu 13 da 430 suka harbu da cutar a kasar, kuma daga cikin su 166 sun mutu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu