Kungiyoyi 15 a Liberia na son gwamnati ta kafa kotun hukunta laifukan yaki
Wasu kungiyoyin fararen hula guda 15 a Liberia, sun gabatar wa majalisar dokokin kasar bukatar ganin an kafa kotun da za ta hukunta masu aikata laifufukan yaki da cin zarafin bil’adama a kasar.
Wallafawa ranar:
Kungiyoyin sun ce lokaci ya yi da ya kamata a kafa wannan kotu a cikin kasar, shekaru 18 bayan yakin basasar da aka gwabza.
Muhawara kan kafa makamantan kotunan dai na ci gaba da fuskantar tarnaki ne tun daga lokacin mulkin shugaba Ellen Johnson Sirleaf da kuma bayan hawa mulkin George Weah a 2018.
Tun a shekarar 2009 wata hukuma ta musamman da kasar ta kafa don hukunta wadanda ke da hannu a aikata laifukan yakin shekaru 18 da suka gabata, ta bukaci samar da kotunan da nufin zartas da hukunci kan mutanen da kungiyoyi da kuma kamfanonin da suka rura wutar yakin basasar kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu