Isa ga babban shafi

'Yan Liberia za su kada kuri'a kan sauya tsarin wa'adin shugaban kasa

Daga zabukan Ghana sai kuma na Liberia, inda a ranar Talata al’ummar kasar za su kada kuri’a a zaben rabar gardama, dangane da kudurin rage adadin shekarun da shugaban kasa ke yi a kowane wa’adi, daga shekaru 6 zuwa 5.

Wasu magoya bayan shugaban kasar Liberia George Weah a birnin Monrovia. 5/12/2020.
Wasu magoya bayan shugaban kasar Liberia George Weah a birnin Monrovia. 5/12/2020. AFP / Zoom Dosso
Talla

Sai dai wasu daga cikin ‘yan adawa na fargabar shugaba mai ci George Weah zai iya amfani da damar wajen tsawaita zamansa kan shugabancin kasar, bayan karewar wa’adinsa.

Yayin zaben raba gardamar, al’ummar Liberian za su kuma yanke hukunci kan kudurin soke dokar da ta haramta musu mallakar takardun zama ‘ya’yan wata kasa baya ga ta su.

A gasar Guinea dai shugaba mai ci Alpha Conde ya samu nasarar zarcewa kan wa’adi na 3 ne bayan yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, kamar yadda takawaransa na Ivory Coast Allassane Ouattara ya yi a baya bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.