Isa ga babban shafi
SAHEL-TA'ADDANCI

Faransa zata janye dakarun ta daga Mali - Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yace kasar sa zata fara rufe sansanonin sojin ta dake arewacin Mali daga karshen wannan shekara, a wani yunkurin na janye dakarun Faransa dake yaki da Yan ta’adda a Yankin Sahel.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron AFP - FRANCOIS MORI
Talla

Macron wanda yake jawabi bayan taron shugabannin kasashen dake cikin kungiyar G5 Sahel a Paris yace za’a fara janye sojojin ne daga watanni 6 na karshen wannan shekara ta 2021 kuma za’a kammala janyewar a karshen shekara mai zuwa ta 2022.

A watan jiya shugaban ya fara gabatar da shirin janye dakarun Faransa 5,100 dake aiki a karkashin rundunar Barkhane dake yaki da Yan ta’adda bayan kwashe shekaru 8 suna taimakawa kasashen dake yankin.

Rundunar Barkhane dake yaki da Yan ta'adda
Rundunar Barkhane dake yaki da Yan ta'adda © AP Jerome Delay

Sai shugaban ya jaddada cewar Faransa zata ci gaba da zama kawa ga rundunar G5 Sahel ta kasashen Mali da Burkina Faso da Chadi da Mauritania da kuma Nijar wadda aka kafa ta domin tinkarar matsalar ‘Yan ta’adda.

Macron yace bayan janye dakarun kasar sa, Faransa zata bar sojojin ta tsakanin 2,500 zuwa 3,000 a Yankin domin fuskantar duk wata barazanar dake iya tasowa.

Shugaban yace burin su itace hana wadannan kungiyoyi Yan ta’adda guda biyu fadada ayyukan su a Yankin sahel da kuma Afirka ta Yamma, yayin da yake cewa ba zasu dauki nauyin da ya rataya akan gwamnatocin kasashen dake yankin ba wajen samar da tsaro da kuma tabbatar da zaman lafiyar jama’ar su.

Dakarun Faransa yayin sintiri a yankin arewacin kasar Burkina Faso.
Dakarun Faransa yayin sintiri a yankin arewacin kasar Burkina Faso. AFP via Getty Images - MICHELE CATTANI

Macron yace abokan gaban su sun janye aniyar su ta fadada yankunan da suke iko da shi ba wai a yankin Sahel kawai ba har ma da Afirka ta Yamma baki daya.

 

Masu sharhi na bayyana cewar rikicin da ake samu na iya yaduwa zuwa kasashen Cote d’Ivoire da Jamhuriyar Benin, abinda ya sa shugaba Macron yace zasu sake nazari domin tinkarar matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.