Nakiya ta raunata dakarun Majalisar Dinkin Duniya 7 a Mali
Dakarun wanzar da zaman lafiya 7 sun ji rauni a tsakiyar Mali a ranar Juma’a, lokacin da motarsu ta taka nakiya da aka samar a gida, a cewar tawagar kiyaye zaman lafiya ta majalisar dinkin duniya.
Wallafawa ranar:
Rundunar kiyaye zaman lafiyar ta Majalisar Dinkin Duhniya ta wallafa a shafinta na Tweeter cewa nakiyar ta fashe a karkashin motar da dakarun ke ciki ne, a yayin da suke kan hanyar zuwa Diallo, a tsakiyar yankin Mopti.
Ba a bayyana kasashen wadanda lamarin ya rutsa da su ba.
Tun daga shekarar 2012 ne ‘yan aware da masu ikirarin jihadi a arewacin Mali suka jefa kasar cikin tashin hankali da ya yi sanadin mutuwar dubban farar hula da mayaka, duk kuwa da taimakon kasa da kasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu