Yunkurin kashe shugaban Mali ba shi da nasaba da ta'addanci - rahoto
Masu bincikie a kasar Mali sun ce yunkurin daba wa shugaba mulkin sojin kasar, Kanar Assimi Goita wuka ba shi da nasaba da ta’addanci.
Wallafawa ranar:
An kai wa Goita hari ne yayin idin Sallah babba, a babban masallacin birnin Bamako a ranar Talata, sai dai maharin bai kai ga yi wa shugaban lahani ba, maimakon haka ya raunata daya daga cikin masu tsaronsa.
Goita wanda ya bayyana kafar talabijin kasar bayan aukuwar al’amarin ya ce yana cikin koshin lafiya, inda ya yi watsi da harin a matsayin wani abin da bai taka kara ya karye ba.
An rantsar da Goita a matsayin shugaban Mali ne bayan da ya kifar da gwamnatin wucin gadi da ya ke aiki a cikinta a matsayin mataimakin shugaba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu