Isa ga babban shafi
MALI-TA'ADDANCI

Yan bindiga sun kashe sojojin Mali 11

Wasu da ake zargin 'yan ta’adda a kasar Mali sun kashe sojojin kasar guda 11, yayin da suka jikkata wasu guda 10 lokacin da suka musu kwantar bauna a Yankin tsakiyar kasar.

Shugaban Mali Assimi Goita
Shugaban Mali Assimi Goita © Crédits : AP
Talla

Rundunar sojin kasar Mali ce ta sanar da kashe sojojin sakamakon wani kazamin harin da ‘Yan ta’adda suka kaiwa dakarun dake sintiri a kusa da Douentza dake Yankin Mopti mai nisar kilomita 600 daga Bamako.

Sanarwar sojin tace an kaiwa tawagar motocin harin ne a safiyar alhamis din nan, inda aka fara tada bam a mota, kafin daga bisani aka budewa tawagar wuta.

Adadin farko ya nuna cewar mutane 11 suka mutu, yayin da wasu 10 suka jikkata, cikin su harda guda 9 da raunin su yayi tsanani.

Sojojin Faransa dake yaki da Yan ta'adda a Mali
Sojojin Faransa dake yaki da Yan ta'adda a Mali AFP - JOEL SAGET

Wani Jami’in sojin Mali ya danganta harin da na Yan ta’adda wadanda suka saba kai hare hare a yankin.

Yankin Mopti na daga cikin inda Yan ta’adda suka fi kai hari a kasar Mali tun bayan barkewar rikicin kasar a shekarar 2012 kafin daga bisani ya watsu zuwa Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso, abinda ya zafafa rikicin kabilanci.

Dubban sojoji da fararen hula suka mutu sakamakon tashin hankalin wanda yayi sanadiyar raba dubban mutane da gidajen su.

Masu tsatsauran ra’ayin dake alaka da kungiyar Al Qaeda sun mamaye yankin sahara na arewacin Mali tun daga shekarar 2012, kafin rundunar sojin Faransa ta Barkhane ta kakkabe su bayan fara aikin ta a watan Janairun shekarar 2013.

Har ya zuwa wannan lokaci wasu yankuna da dama na hannun Yan ta’addan dake dauke da makamai duk da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla a shekarar 2015 domin samar da zaman lafiya a cikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.