Isa ga babban shafi
MALI-SIYASA

Kotun ECOWAS ta bukaci Goita yayi bayani akan tsare tsoffin shugabannin Mali

Kotun kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ta bukaci gwamnatin Mali tayi bayani akan yadda ta tsare tsoffin shugabannin kasar Moctar Ouane da Bah Ndaw.

Shugaban Mali Assimi Goita
Shugaban Mali Assimi Goita MALIK KONATE AFP/File
Talla

Wani lauya tare da wasu Yan kasar Mali guda 2 suka gabatar da kara inda suke bukatar kare tsoffin shugabannin biyu wadanda aka nada shugaban kasa da Firaminista domin jagorancin gwamnatin rikon kwarya bayan juyin mulkin da Kanar Assimi Goita ya jagoranta a watan Agustan bara.

A watan Mayun da ya gabata Goita ya kifar da gwamnatin Ouane bayan garambawul da aka yiwa majalisar ministocin kasar, inda ya bayyana kan sa a matsayin shugaban kasa.

Ya zuwa yanzu babu wanda ya san inda tsoffin shugabannin biyu suke, sai dai ana zargin cewar sojojin na tsare da su a gidajen su.

Tsohon shugaban rikon kwarya Bah N'Daw tare da Goita
Tsohon shugaban rikon kwarya Bah N'Daw tare da Goita AP

Lauyan dake kare tsoffin shugabannin Mamadou Ismaila Konate ya sanar da cewar sun bukaci kotun ECOWAS da ta bukaci shugaban kasar da ya bayyana inda ake tsare da mutanen biyu nan da ranar 28 ga wannan watan.

Karar ta kuma bukaci gwamnatin Mali da ta baiwa tsoffin shugabannin biyu ‘yancin gudanar da harkokin su na yau da kullum ba tare da sanya musu wani shinge ba.

Taswiran Mali
Taswiran Mali Manel MENGUELTI AFP

Goita yayi alkawarin gudanar da zaben shugaban kasa a watan Fabarairu mai zuwa, amma ana fargabar ko zai iya cika alkawarin da ya yiwa jama’ar kasar da kuma shugabannin kungiyar ECOWAS cikin kankanin lokacin da ake da shi.

Gwamnatin Mali na ta fafutukar murkushe Yan ta’addan da suke kai munanan hare hare suna kasha mutane tun daga shekarar 2012, abinda ya kaiga rasa iko da wani sashe na kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.