Isa ga babban shafi
Kamaru

Kamaru na shirin korar wasu kungiyoyin agaji na kasa da kasa

Gwamnatin Kamaru ta bai wa kungiyoyin agaji da masu zaman kansu na kasahen ketare wa’adin wata daya don sake yin sabuwar rejista matukar dais una bukaci ci gaba gudanar da ayyukansu a cikin kasar.

Wasu 'yan Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya dake gudun hijira a Kamaru, yayin da suka yi layi don karbar tallafin abinci.
Wasu 'yan Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya dake gudun hijira a Kamaru, yayin da suka yi layi don karbar tallafin abinci. UNHCR / C. TIJERINA
Talla

Daga cikin abubuwan da gwamnati ke bukatar kungiyoyin su gabatar sun hada da takardun shaidar kafuwarsu, da illahirin ma’aikatan da ke karkashinsu da kwantaragin albashin ma’aikata da dai sauransu.

Ministan tsaron cikin gidan kasar, Paul Atanga Nji, ya bayyana dalilan daukar matakin.

Da zarar aka fahinci cewa kungiyoyi na aiki ba tare da mutunta dokoki ba, dole ne mu dauki matakin dawo da sua kan tsari, abin da ke faruwa kenan a yau.

Yanzu haka akwai kungiyoyin da yawansu ya kai 30 zuwa 40  na fama da matsaloli wajen gabatar da rahoton ayyukansu a karshen shekara, to dole ne mu dauki mataki, duk da cewa akwai wadanda ke ayyukansu a kan ka’ida.

Abu na farko da muke yi shi ne jan hankali ga wadannan kungiyoyi da kuma wayarda kawunan wadanda ke tafiyar da su, daga nan kuma za mu dauki matakin ladaftarwa a kan wadanda ke karya dokokin kasar Kamaru. Irin wadannan ba abin da za su yi face tattara nasu ya nasu domin barin wannan kasa ta Kamaru.

Ya zama wajibi mu sanya ido game da abubuwan da suka yi.

Kasar Kamaru dai na fama da tashe tashen hankula da suka hada da Boko Haram a arewacin kasar da kuma 'yan aware masu neman ballewa domin kafa jamhuriyar Ambazonia a yankunan kasar biyu da ake amfani da turancin Ingilishi wato Arewa maso Yamma da kuma Kudu maso Yamma, wanda ya haifar da rasa dumbin rayuka da dukiyoyi tare da raba dubbai da gidajensu.

Karuwar bukatar agajin jinkai ya samar da kungiyoyi masu zaman kansu na kasa da kasa a Kamaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.