Isa ga babban shafi
Guinea - Juyin mulki

MDD ta yi Allah wadai da juyin mulki a Guinea Conakry

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yayi Allah wadai da amfani da karfin da sojoji suka yi a Guinea wajen kwace mulki, inda ya bukace su da su gaggauta sakin shugaban kasar Alpha Conde.

Sojojin Guinea a birnin Conakry 5/09/21.
Sojojin Guinea a birnin Conakry 5/09/21. AFP - CELLOU BINANI
Talla

Sanarwar da Guterres ya gabatar ta ce yana sanya ido akan abinda ke faruwa a Guinea sau da kafa, yayin da ya bayyana takaicin sa na amfani da karfin bindiga wajen kwace iko.

Yanzu haka al'umaran yau da kullum sun tsaya cik a birnin Conakry, inda aka rufe kasuwanni da manyan shaguna, bayan sanarwar sojojin kasar wadanda suka yi ikrarin juyin mulki tare da kama shugaba kasa Alpha Conde, duk da cewa a bangare guda gwamnati ta ce ta murkushe yunkurin ne.

Hafsan sojin da ya bayyana a kafar talabijin din kasar ya kuma sanar da rufe iyakokin sama da kasa da kuma rusa gwamnatin kasar.

Ita ma gwamnatin Najeriya tayi Allah wadai da juyin mulkin inda ta bukaci mayar da halartacciyar gwamnatin kasar ba tare da bata lokaci ba.

Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta gabatar mai dauke da sanya hannu Esther Sunsuwa tace juyin mulkin ya sabawa dokokin kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ta ECOWAS.

Najeriya tace ta kadu da juyin mulkin inda ta bukaci sojojin da suka kifar da gwamnatin da su dawo da doka da oda a cikin kasar ba tare da bata lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.