Isa ga babban shafi
Mali - Ta'addanci

Harin ta'addanci ya hallaka Sojojin Mali 5

Ma’aikatar tsaron Mali ta tabbatar da kisan da ‘yan bindiga suka yiwa Sojin kasar 5 a wani farmaki kansu jiya Lahadi.

Wasu Sojin Mali a yaki da 'yan ta'adda.
Wasu Sojin Mali a yaki da 'yan ta'adda. MICHELE CATTANI AFP/File
Talla

Sanarwar da ma’aikatar tsaron ta fitar ta ce tawagar dakarun Sojin kasar da ke sintiri a Macina sun mayar da martani kan wani farmakin ‘yan ta’adda da tsakar ranar jiya lahadi wanda ya kai ga kisan Sojin 5.

Sanarwar ta bayyana cewa, dakarun suma sun yi nasarar hallaka mayakan ta’addancin 3 tare da kone motar su ko da ya ke suma sojin sun yi asarar motocinsu guda 5.

Sa’o’I kalilan bayan sanarwar Ma’aikatar tsaron ta Mali ita rundunar Majalisar dinkin duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar MINUSMA ta sanar da jikkatar dakarunta 3 wadanda ta ce sun samu rauni ne bayan taka wani abin fashewa gab da sansaninsu da ke Kidal.

Yankin arewa maso gabashin Mali na ci gaba da fuskantar hare-haren ta’addanci tun bayan yunkurin mayaka masu ikirarin jihadi a shekarar 2012 da ke neman ‘yancin kansu.

Zuwa yanzu dubunnan fararen hula suka rasa rayukansu galibi mata da kananan yara yayinda dakarun Soji dubunnai suka kwanta dama a yaki da mayakan masu ikirarin jihadi da suka mamaye arewacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.