Firaministan Somali ya yi watsi da batun dakatar da ikonsa
Firaminstan Somalia Muhd Hussein Roble yayi watsi da matakin da shugaban Somalia Muhd Abdul Farmajo ya dauka na dakatar da ikon zartaswar sa abinda da ya kara munin rikicin siyasar kasar.
Wallafawa ranar:
Shugaba Mohamed Abdul Mohamed, da aka fi sani da Farmaajo ya dauki matakin ne duk da kokarin 'yan siyasar Somalia na sasanta rikicin da ke ta'azzara tsakanin sa da Firaminista Mohamed Hussein Roble.
Farmajo ya zargi Firaministan sa ne da sabawa kundin tsarin mulkin kasa da kuma daukar matakai marasa kan gado wanda zai iya share fagen rashin zaman lafiya a Somalia ta fuskokin tsaro da siyasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu