Isa ga babban shafi
Kamaru

Kungoyin kare hakkin bil'adam sun bukaci Kamaru da saki 'yan adawa dake tsare

A kasar Kamaru, yayin da ake bukin tunawa da magobaya bayan jam’iyyar MRC mai adawa da suka kwashe shekara guda tsare a kurkuku sakamakon gudanar da zanga-zanga, kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasa da kasa ciki harda Human Rights Watch da Amnesty International sun bukaci gaggauta sakin mutanen 124 dake tsare.

Wasu jami'an tsaron kasar Kamaru a garin Buea.
Wasu jami'an tsaron kasar Kamaru a garin Buea. © Marco Longari/AFP
Talla

A ranar 22 ga watan Satumbar bara ne jami’an tsaron Kamaru suka tarwasa gungun masu zanga-zangar neman murabus din shugaban kasar Paul Biya mai shekaru 88 da ya mulki kasar kusan shekaru 40.

Jami’an tsaro sun yi amfani da barkwanon tsohowa da kuma ruwan zafi wajen tarwasa magoya bayan jam’iyyar MRC kafin kame sama da mutane 500.

Yanzu haka sama da 124 na tsare a gidajen yari daban-daban na kasar ta Kamaru, wasu daga cikinsu basu taba zuwa kutu ba cikin watanni 12 da suka yi suna tsare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.