Isa ga babban shafi
Algeria - Faransa

Algeria ta janye jakadanta na Faransa

Algeria ta janye jakadanta dake kasar Faransa, Mohammed Antar Daoud sakamakon rashin jituwa dake kara tsananta a tsakanin kasashen biyu.

Shugaban Algeria, Abdelmajid Tebboune.
Shugaban Algeria, Abdelmajid Tebboune. AFP - -
Talla

Wannan kuwa na zuwa ne bayan da shugaban Faransa Eammanuel Macron  ya cacaki wata jaridar kasar mai suna Le Monde da ta wallafa labarin cewa Faransar ta yi wa Algeriar Mulkin mallaka cikin Zaluci abin da ya yi wa Algerian zafi.

Da take karin bayani kan janye jakadan, fadar shugaban kasar Algeria ta ce nan gaba kadan zata fitar da sanarwa wadda cikinta zata mayarwa da shugaban Faransan zazzafan martani.

Matakin na Algeria na zuwa ne a daidai lokacin da ake zaman tankiya tsakanin kasashen biyu, biyo bayan matakin Faransa na rage yawan bizar da take bai wa ‘yan Algeria, Morocco da Tunisia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.