Majalisar rikon kwaryar Libya ta dakatar da ministan harkokin waje
Majalisar rikon kwaryar kasar Libya ta dakatar da Ministar harkokin wajen kasar Najila Al Mangoush daga mukamin ta, biyo bayan zargin daukar wasu matakai ba tare da ta samu amincewar ta ba.
Wallafawa ranar:
Matakin dakatar da wannan jami’ar diflomasiyar na zuwa ne yayin da suka rage kasa da mako guda a gudanar da babban taro dangane da makomar kasar ta Libya.
Majalisar rikon kwaryar kasar ta kaddamar da bincike don tattance gaskiyar tuhumar da ake yiwa Najla AlMangoush, inda wata majiya ke nuna cewa kalaman ta na bayyana aniyar hukumomin Libya na tattaunawa da Amurka domin tasa keyar daya daga cikin mutanen da ake zargin yana da hannun a harin jirgin saman Lockerbie.
Hukumomin Libya sun haramtawa Mangoush izinin fita daga kasar yanzu haka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu