Rikicin Sudan ya sauya salo bayan arangamar 'yan sanda da masu zanga-zanga
Rikici ya sake barkewa a tsakar birnin Khartoum na Sudan yau Alhamis kwana guda bayan jami’an tsaro sun kashe masu zanga-zanga 15 a wani yanayin tashin hankali da kasar ke ci gaba da gani tun bayan sake karbe ikon sojoji a ranar 25 ga watan jiya.
Wallafawa ranar:
Daga daren jiya laraba ne rikicin ya faro bayan da jami’an tsaron suka rika harba hayaki mai sanya hawaye kan masu zanga-zangar adawa da mulkin Soji a arewacin birnin na Khartoum fadar gwamnatin Sudan da nufin tarwatsa su, sai dai kuma zanga-zangar ta juye zuwa rikici tare da sake yin muni a yau.
Bayanai sun ce a yau alhamis jami’an tsaron sun kara matse yankin da masu zanga-zangar ke bore ta hanyar kara shingaye don nufin hanasu fadada boren zuwa wasu yankuna.
Tuni dai matakin jami’an tsaron na Sudan kan masu zanga-zangar da ya kai ga kisan mutane 15 ya haddasa caccaka daga kasashen duniya kan gwamnatin kasar dai dai lokacin da rikicin ke ci gaba da munana.
Rahotanni sun ce mutanen da ke cikin zanga-zangar ta yau ya ninka wadda aka gani a baya, yayinda gwamnati ta yi umarnin girke tarin jami’an tsaro don hana su tasiri.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu