Isa ga babban shafi
Somalia

Mutane 8 sun mutu a harin da Al-Shabaab ta kai Somalia

Mutane 8 sun mutu, da dama sun samu raunuka  bayan da wata mota da aka dana wa abin fashewa ta yi bindiga a kusa da wata makaranta a mogadishu, babban birnin Somalia, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana.

Kakakin rundunar 'yan sandan Somalia ya ce fararen hula 8 sun mutu, 17 sun samu rauni a fashewar.
Kakakin rundunar 'yan sandan Somalia ya ce fararen hula 8 sun mutu, 17 sun samu rauni a fashewar. - AFP/File
Talla

Kungiyar Al-shabaab ta dauki alhakin wannan harin na baya bayan nan a kasar da rikici ya wa dabaibayi, inda ta ce ta nemi hargitsa wasu mutane da ke karbar horon soji ne.

Jami’in tsaro, Mohamed Abdillahi ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa tun da farko cewa fashewar ta tashi ne daga wata mota inda har dalibai 11 suka samu rauni.

Shaidu sun ce wani ayarin motoci dauke da sojojin kiyaye zaman lafiya na Tarayyar Afirka  da ke yaki da ‘yan ta’adda na wucewa ta hanyar a lokacin da fashewar ta auku.

sun ce fashewar ta haddasa mummunar barna ga makarantar da kuma ababen hawa da aka ajiye a kusa da ita.

Kungiyar da ake alakanta da Al-Qaeda tana yawan kai hare hare a babban birnin kasar da sauran yankunanta, inda a kwanan nan ne ma suka kai hari kan fitaccen dan jaridar Somalia suka kashe shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.