Isa ga babban shafi

An gudanar da zaben wakilan yankuna a Algeria

A Algeria sama da mutane milyan 23 ne suka karbi katunan zaben  wakilan hukumomi da na jihohi da ya gudana yau asabar.

Zaben Algeria
Zaben Algeria REUTERS - RAMZI BOUDINA
Talla

Zabe dake da matukar tasiri ga hukumomi kasar,da kuma zai bayar da damar canza salon siyasa tun bayan kawar da tsohuwar gwamnatin  marigayi Abdel Aziz Bouteflika da ya shugabanci kasar ta Algeria.

Shugaban kasar Algeria Abdel Madjid Tebboune
Shugaban kasar Algeria Abdel Madjid Tebboune AFP - -

Shugaban kasar mai ci Abdel Madjid Tebboune tareda rakiyar iyalan sa da wasu daga cikin mukaraban gwamnatin sa ,sun kada kuri’un su a wannan zabe dake a matsayin zakaran gwajin dafi .

Wasu daga cikin hotunan yan Takara a Algeria
Wasu daga cikin hotunan yan Takara a Algeria AFP - -
Ga baki daya  hukumar zaben kasar ta bayyana cewa yan takara 15.230 ne suka tsayar da takarar su a zaben da ake da kujerun wakilai  1541,yayinda yan takara 18.910 suke neman kujerun wakilan jihohi 58.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.