Isa ga babban shafi

Yan ta'adda sun kashe sojojin Jamhuriyar Benin biyu a yankin Pendjari

A wani hari da 'yan ta'adda suka kai yankin arewacin Jamhuriyar Benin ,sun hallaka sojojin kasar biyu tareda raunata wasu daban.Wannan ce sanarwar da hukumomin kasar ta Benin suka fitar kusan kwana daya da kai harin a yankin Pendjari dake daf da kan iyaka da kasar Burkina Faso.

Yankin Pendjari a Jamhuriyar Benin daf da kan iyaka da Burkina Faso
Yankin Pendjari a Jamhuriyar Benin daf da kan iyaka da Burkina Faso STEFAN HEUNIS / AFP
Talla

Wannan dai ne karo na biyu da yan ta'adda ke kaddamar da hari a Jamhuriyar Benin,yayinda gwamnati a karkashin shugabancin Patrice Talon ta sanar da canza salon ayukan tsaro a kan iyakokin kasar da Burkina Faso.

Pendjari.net
Pendjari.net Source : http://www.pendjari.net/IMG/jpg/limites.jpg\\n

A arewacin kasar, rahotanni na nuni cewa jama'a na gudanar da harakokin su ba tareda fuskantar tsaiko, yayinda wasu yan kasar ka fatan ganin hukumomin sun taka muhimiyar rawa don tabbatar da tsaro a wannan yankin ga bakin daya.

Jami'an tsaro a Jamhuriyar Benin
Jami'an tsaro a Jamhuriyar Benin AFP - YANICK FOLLY

Shugaban kasar Patrice Talon ya umurci babban hafsan sojan kasar da tsaurara matakan tsaro da bincike a cikin kasar.

Issiakou Ibrahim Madougou wani mazauni kasar ta benin ya bayyana mana halin da ake ciki yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.