Isa ga babban shafi
MOROCCO

Ana tuhumar malaman jami'a 4 da bukatar lalata domin bada maki

Hukumomin Kasar Morocco sun gurfanar da wasu malaman jami’a guda 4 saboda tuhumar da ake musu na baiwa dalibai mata maki mai kyau domin yin lalata da su.

Sarki Mohammed na Morocco
Sarki Mohammed na Morocco AFP PHOTO/FADEL SENNA
Talla

Ita dai wannan badakalar an bankado ta ne a watan Satumba, lokacin da kafofin yada labaran kasar suka samu tsegumi ta hanyar kafar sada zumunta wadda ke dauke da tattaunawa tsakanin malaman da daliban su.

Hudu daga cikin malaman wadanda ke koyarwa a Jami’ar Hassan dake Settat kusa da birnin Casablanca na fuskantar tuhumar lalata da nuna banbancin jinsi da kuma cin zarafin mata.

Bayan zaman kotun na yau Talata, alkalin kotun ya dage shari’ar zuwa 14 ga wata, yayin da ya bayar da umurnin tsare guda 3 daga cikin su a gidan yari.

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace a shekarun baya irin wannan badakala a Jami’oin Morocco sun girgiza kasar amma kuma babu wanda aka gurfanar a kotu.

Kungiyoyin fararen hula sun ce an samu karuwar cin zarafin mata a kasar, sai dai yanayin kasar na hana matan da aka ci zarafin su gabatar da kara a gaban hukuma saboda fargabar tsangwama da kuma bata suna.

A shekarar 2018 majalisar dokoki ta amince da wata dokar hukunta wadanda aka samu suna cin zarafin mata, amma duk da haka dokar bata aiki yadda ya dace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.