Majalisar Sojin Guinee ta mayarwa iyalan Sekou Toure da kadarorin su
Gwamnatin sojin kasar Guinee ta mayarwa iyalan shugaban kasar na Farko marigayi Sekou Toure da wasu daga cikin kadarorin sa da aka kwace yau sama da shekaru 30.
Wallafawa ranar:
Mai dakin tsohon Shugaban kasar Andree Toure mai shekaru 87 a yau, ta bayyana farin cikin ta duk da cewa ,yan lokuta bayan mutuwar Ahmed Sekou Toure shugaban kasar a lokacin ,ta fuskanci dauri gidan yari na shekaru hudu,kafin ta samu ficewa daga kasar bayan da aka sako ta.
Ana dai kalon tsohon Shugaban kasar marigayi Ahmed Sekou Toure a matsayin jarumi da ya taka muhimiyar rawar wajen kare murradun kasar daga turawan mulkin malaka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu