Isa ga babban shafi
Kamaru

Kotun Kamaru ta daure 'yan adawa 47

Kotu a kasar Kamaru ta yanke hukuncin dauri kan magoya bayan madugun ‘yan adawar kasar Maurice Kamto su 47, ciki har da mai magana da yawunsa da kuma ma’ajin kudi na jam’iyyarsa, saboda samunsu da laifin yi wa kasar tawaye.

Jagoran 'yan adawar Kamaru Maurice Kamto tare da magoya bayansa.
Jagoran 'yan adawar Kamaru Maurice Kamto tare da magoya bayansa. REUTERS/Zohra Bensemra
Talla

Hukunce-hunkuncen dai sun kama ne daga daurin shekara 1 zuwa 7 a gidan Yari, kamar dai yadda wani kusa a jam’iyyar adawa MRC ta Maurice Kamto ya sanar.

Su dai wadannan mutane 47 da aka yanke wa hukuncin daurin, an kama su ne tun ranar 22 ga watan Satumban shekarar 2020, lokacin da jam’iyyarsu da wasu jam’iyyun adawa suka shirya zanga-zangar adawa da shugaba Paul Biya wanda ke kan karagar mulkin kasar ta Kamaru yau shekaru 39.

A wancan lokaci, ‘yan sanda sun yi amfani da karfi domin tarwatsa tarzomar musamman ma a birnin Douala, inda suka cafke sama da mutane 500, kuma yanzu haka 124 daga cikinsu na tsare, a cewar jam’iyyar ta MRC.

Kakakin babbar jam’iyyar adawar, Olivier Bibou Nissack da ma’ajin kudin jam’iyyar Alain Fogue na daga cikin wadanda kotun sojin da ta yi zamanta a birnin Yaounde ta daure.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.